Jam’iyyar NNPP a Najeriya ta ce jagoran jam’iyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba zai koma cikin jam;iyyar APC ba.

A wani saƙo da jamiyyar ta fitar na martani ga furcin sabon shugaban jam’iyyar APC Abduahi Ganduje, mai binciken kudi na jam’iyyar Ladipo Johnson ya bayyanawa manema labarai ya ce za su mai da hankali wajen dinke barakar da ke cikin jam’iyyarsu.
Ya kara da cewa jagoran jam’iyyar NNPP ya tserewa Dakta Abduah Ganduje a siyasa,domin haka a yanzu kwankwas ba shi da lokacin saurarn jam’iyyar.

Ya ce a halin yanzu ya mayar da hankali ne wajen samar da cigaba a ciikin njamiyyarsu, sannan jamiyyar ta yi mamaki da aka baiwa Gandje shugaban jam’iyya.

Idan ba a manta ba Dakta Abdulahi Ganduje ya bukaci sanata Rabi’u Kwankwas da ya koma ciin jam’iyyar APC domiin a yanzu shi ne da wuka da nama a cikin jam’iyyar.
Ganduje ya bayyana haka ne a cikin jawabin da yayi yayin ganawa da manema labarai bayan zabarsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
