
Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta ce zata ci gaba kama yaran da shekarunsu bai kai 18 ba waɗanda suke tuƙa Baburin Adaidai Sahu.
A wata sanarwa da kakakin hukumar Nabulisi Abubakar K/Naisa ya sanyawa hannu, ya ce Shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka, lokacin da yake karbar baƙuncin gamayyar ƙungiyoyin Adaidai Sahu na jihar nan, ƙarƙashin jagorancin Alh. Mansur Tanimu

Engr. Faisal ya ce Hukumar KAROTA ba za ta lamunci bawa ƙananan yara wandanda shekarunsu bai kai 18 ba tuka Adaidai Sahu

Haka kuma, Hukumar ba za ta yadda da yin amfani da waya a lokacin tuki ba, da kuma ɗaukar kayan da suka wuce kima a cikin Adaidai Sahu
A nasa jawabin Shugaban Gamayyar Ƙungiyar Adaidaita Sahu ta jihar Kano Alh. Mansur Tanimu ya ce sun zo Hukumar KAROTA ne domin taya murna ga sabon shugaba tare da alkawarin bayar da haɗin kai domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba
Ya bayar da tabbacin bawa Hukumar KAROTA haɗin kai domin ciyar da jihar Kano gaba
A wani cigaban kuma, shugaban Hukumar ya karɓi baƙuncin kungiyar Adaidai Sahu ta Kwankwasiyya kar ƙarƙashin jagorancin Comr. Nazifi BK Gidan Kuɗi,
Sun roƙi Gwamnatin jihar Kano ta samar da makaranta wadda za ta dinga bayar da horo ga matuƙa Baburan Adaidai Sahu na faɗin jihar nan hakan zai taimaka wajen rage yawan aikata laifukan tuki titinan jihar nan
A ƙarshe ya roƙi ƙungiyoyin Adaidai Sahu na jihar Kano da su zama haɗa kansu domin ciyar da jihar Kano gaba
Shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir
Ya karbi baƙuncin ƙungiyoyi daban daban wadanda suka zo domin ƙulla alaƙar aiki da Hukumar KAROTA.