Al’ummar ƙaramar hukumar Guma a jihar Benue sun tashi da zanga-zanga a babbar hanyar Makurɗi zuwa Lafia sakamakon kisan gillar da aka yi wa wasu mutane.

Maza da matasa da matasa ne su ka dugunzuma tare da tare babbar hanyar bayan da aka hallaka mutane boyar a ƙauyuka biyu na jihar.
An hallaka mutane uku a ƙauyen Ngban a ranar Alhamis yayin da aka kashe wasu mutane biyu a ƙauyen Nyian a safiyar yau Juma’a.

Mutanen sun koka a kan yadda aka hallaka mutane sama da 30 a ƙauyen da ya zame musu tudun mun tsira amma ake bi ana kashewa.

Masu zanga-zangar sun ce sun fita tun ƙarfe 5:00am na asubahin yau Juma’a tare da bin babbar hanyar Makurɗi zuwa Lafiya domin nuna rashin jin daɗinsu a dangane da yadda ake musu kisan gilla.
Mutanen sun nuna rashin gamsu da yadda tsarin tsaro a jihar ke gudana har su ka buƙaci gwamnan jihar sai ya yi musu bayani a kan halin da su ke ciki da kuma matakin da zai ɗauka a kai.
Har lokacin da mu ke kammala wannan labari mahukunta ba su ce komai a dangane da lamarin ba.