Majalisar ɗinkin duniya ta ce akwai mutane aƙalla sama da miliyan 20 da ke fama da matsananciyar yunwa a ƙasar Sudan.

Ƙididdigar da majalisar ta fitar a yau Juma’a ta ce hakan ya faru ne sakamakon rikicin da ke faruwa a ƙasar.
Tun bayan ɓarkewar rikicin a watan Afrilu, rikicin na ci gaba da yaɗuwa a ƙasar wanda hakan ya haddasa ƙaruwar yunwa a ƙasar.

Wakilan majalisar ɗinkin duniya da ke lura da harkokin abinci a ƙasar Sudan sun ce hakan ya janyo matsananciyar rayuwa a ƙasar.

Rikici ya fara a ƙasar Sudan bayan da kawunan manyan sojin ƙasar ya rabu biyu bayan da su ka karɓi mulki daga hannun farar hula a shekarar 2021.
Sakamakon rikicin da ke faruwa a ƙasar wata ƙididdiga ta nuna cewar za a fuskanci ƙarancin abinci sanadin rashin wadataccen noma da ba a yi ba a ƙasar sakamakon rikicin.