Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana cewa aƙalla Jihohin Najeriya 19 ne za su fuskanci mamakon ruwan sama da zai iya janyo musu ambaliyar ruwa.

Ko’o’dinetan hukumar na Jihar Legas Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Farinloye ya ce daga cikin Jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwan sun hada da Delta, Ekiti, Ondo, Legas, Anambra, Ogun da kuma Nasarawa.

Sauran sun hada da Kuros Riba, Bauchi, Jigawa, Osun Kwara Zamfara, Sokoto, Adamawa, Taraba, Benue, Imo, da kuma Jihar Abia.

Nema ta ce Jihohin za su iya fuskantar ambaliyar ne a watan August da muke ciki.