Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ta bakin mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka yayin ganawa da ƴan jaridar fadar shugaban ƙasa.

Ya ce shugaban Najeriya ba shi da niyyar ƙara farashin man fetur saɓanin yadda ake yaɗa jita-jitar hakan a kafofin sa da zumunta.

Ya ƙara da cewa a wannan lokaci ana ƙoƙarin daidaita farashin man fetur ɗin maimakon cigaba da ƙara farashinsa a gidajen mai.

Ajuri ya ce duk da tsadar man fetur da ake fuskanta a halin da ake ciki, Najeriya na sahu gaba cikin ƙasashen Afrika da ake siyar da man fetur cikin sauƙi.

An fara farfagabar ƙaruwar farashin litar man fetur ne tun bayan da farashin dalar amuruka ta fara hauhawa a kasuwar bayan fage a Najeriya.

Sai dai kamfanin mai a Najeriya NNPC ya ce ba shi da niyyar sake ƙara farashin litar man daga naira 617 da ake siyarwa.

Batun da dillalan man fetur su ka koka a dangane da haka.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: