Fadar shugaban Kasa a Najeriya ta bayyana cewa shugaban Kasa Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin mai zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki.

Babban sakateren gwamnatin tarayya Dr George Akume ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Sakataren ya ce za a rantsar da sabbin ministocin ne a filin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja da misalin karfe 10:00 na safiya.

Sanarwar ta ce ministocin da za a rantsar kowanne zai je da mutum biyu a matsayin bakinsa.

Sannan kowamne minista da bakin da aka gayyata su kasance a zaune a dakin taron da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: