Aƙalla mutane biyu ne su ka rasa rayuwarsu yayin da sama da mutum 30 su ka jikkata a sanadin rushewar wani gini a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a Abuja Abbas Idris ne ya bayyana haka yayin a yake yi wa ƴan jarida ƙarin haske dangane da rushewar ginin.
Lamarin ya faru a yau Alhamis a Lagos Cresent da ke unguwar Garki ll.

An tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da aka garzaya da mutane 35 zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayar da umarnin gaggawa don ganin an tabbatar da kama mammalakin gidan.

Ya ce wajibi ne a kamoshi domin ana zargin ginin ma an yi shi ne ba bisa yarjewar hukumomin gwamnati ba.
Ministan dai ya sha alwashin tsaftace gine-gine a Abuja yayin da ya bayar da umarnin rushe wasu gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba har guda 6,000.