Wata kotun shari’ar musulunci a Kano ta aike da wani magidanci zuwa gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi bisa zargin dukan tsohuwar matarsa.

Mutumin mai suna Sulaiman Shu’aibuu mai shekaru 46 a duniya zai zauna a gidan gyaran hali har zuwa ranar 7 ga watan Satumba mai kamawa.
Tsohuwar matar mutumin ce dai ta yi ƙarar mutum a wajen jami’an tsaro take da’awar ya yi mata duka tare da iƙirarin ɓata mata suna.

Alƙalin kotun mai shari’a Nura Yuusuf Ahmad ne ya bayar da umarnin ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali da tarbiyya.

A ranar Litinin matar ta yi ƙorafi a wajen jami’an tsaro.
Matar mai suna Adama ta yi ƙorafin tsohon mijin nata ya sameta a ranar 18 ga watan Agustan da mu ke ciki da daddare yayin da ta ke zarce da wani saurayinta kuma ya daketa tare da ɓata mata suna a matsayinta na mace.
Zargin da ya saɓawa sashe na 165 da kuma sashe na 188 na kundin shari’ar jihar Kano.