Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani likita da ke aiki a asibitin koyarwa na mallam Aminu Kano.

An kama Dakta Bashir Zubairu a yayin hanyarsa ta zuwa jihar Kogi domin halartar addu ar kwanaki 40 na rasuwar mahaifiyarsa.
Rahotannin da muke samu a yanzu shi ne waɗanda suka yi garkuwa da shi sun buƙaci a basu kuɗi naira miliyan 200.

Idan ba a manta ba a Ranar Talata aka ceto Magajin garin daura wanda aka yi garkuwa da shi watanni biyu da suka gabata.
