Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na farko bayan darewarsa karagar mulki.

Wannan shi ne karo na farko da sabbin ministocin da ya nada su ka halarci zamam bayan da aka rantsar da su a makon da ya gabata.
Sanatoci 45 shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar bayan da majalisar dokoki ta ƙasa tantancesu.

A zaman majalisar zartarwa da ya gudana a yau akwai mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kaashim Shatima, da sakataren gwamnatin tarayya.

Sauran su ne shugaban ma’aikatan Najeriya, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya sai ministocin da ya rantsar a makon da ya gabata.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sabbin ministocin da su kasance masu yin aiki da gaskiya tare da ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.