Rundunar yan sanda a jihar Jigawa sun samu nasarar kama wasu mutane shida daga ciki har da wanda ke safarar makamai.

 

Daga cikin mutane shida akwai wani Yusuf A Yusuf da Bilal Faraji ɗan ƙasar Nijar.

 

Mutane biyu na safarar makamai , sataar babura da kuma barnar kayan gwamnati.

 

Mukaddashin kakakin yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da haka bayan aikewa da Matashiya TV sanarwar a ranar Talata.

 

Ya ce mutane biyun ƴan ƙasar Nijar na yin aika-aikar ne a a yankin ƙaramar hukumar Ringim a jihar.

 

Bayan bincike d asu ka yi sun gano mutanem na siyar da makamai tare da safarsu tsakanin jihohin Kano, da Jigawa.

 

Rundunar ta ce ta kama makamai da kuma kuɓutar da babur guda da wayoyin hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: