Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas ya bukaci da a turawa jihar ƙarin jami’an tsaron soji a jihar domin kwato guraren da ‘yan bindiga su ka mamaye a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai wa babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Laraba.


Gwamnan ya ce ‘yan ta’addan su na cin karansu babu babbaka a wasu yankunan Jihar, inda suka mayar da wasu guraren muhallin zamansu.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa bayan turawa jihar Jami’an tsaron, zai samar musu da duk wani abinda suke bukata bayan sun isa jiharsa.
A yayin jawabinsa babban hafsan sojin na kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi alkawarin tura karin dakarun soji zuwa Jihar ta Taraba.
Sannan ya ce nan ba da dadewa ba za a tura karin jami’an tsaron Jihar, domin kulawa da rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar.