Magoya bayan jam’iyyar Labour Party da dama ne a Jihar Kogi su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC a Jihar.

Shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 21 ne suka sauya sheƙar zuwa jam’iyyar ta APC a Jihar.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa shugabannin Jam’iyyar ta LP sun koma jam’iyyar ta APC ne tare da dumbin magoya bayansu a ranar Juma’a.

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Abdullahi Bello shine ya karbi wadanda suka sauya shekar zuwa Jam’iyyar.

Alhaji Bello ya bayyana cewa jam’iyya APC jam’iyya ce mai tabbatar da daidaito da kyautatawa wadanda suka hidimta mata.

Shugaban ya kuma bayyana farin cikinsa bisa komawar su cikin jam’iyyar, tare da tabbatar musu da cewa za su hada hannu da su domin cimma dukkan wata nasara a jam’iyyar.

A yayin jawabin shugaban masu sauya shekar Awe Kayode ya ce sun yanke hukuncin komawa jam’iyyar ta APC ne domin goyon bayan dan takarar gwamna a Jam’iyyar Usman Ododo a zaben gwamna wanda za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Kayode ya kara da cewa sauya shekar tasu ta zama tilas ne a lokacin da suka fahimci cewa jam’iyyar ta Labour ta rasa madafa a fadin Jihar ta Kogi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: