Ma’aikatan majalisun dokokin Jihohin Najeriya PASAN sun yi barazanar tsunduma yajin aiki daga gobe Laraba.

Kungiyar Ma’aikatan sun kudiri aniyar tafiya yajin aikin ne sakamakon rashin bai’wa majalisun ’yancin gudanar da kudadensu da gwamnoni suka yi.

Jaridar Daily Trust ta ce ma’aikatan su na neman gwamnonin jihohin da su bar majalisun su fara cin gashin kansu suma.

Kazalika kungiyar ta bayyana cewa mambobinta za su rufe ofisoshinsu, har sai lokacin da gwamnonin su ka gaggauta bai’wa majilisun damar ’yancin gudanar da kudadensu, kamar yadda kudin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya tanada.

A wata wasika da ma’aikatan suka aike wa da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, shugaban ƙungiyar shugabannin majalisun dokokin Jihohi, da kuma jami’an tsaron farin kaya ta DSS, takardar ta bayyana cewa shiga yajin aikin ya zama dole, matukar wa’adin da suka bai’wa gwamnonin ya cika ba su yi komai ba akan lamarin.

Kungiyar ta ce a baya sun bai’wa gwamnonin wa’adin makonni uku domin su bar majalisun su ci gashin kansu ko kuma su shiga yajin aikin.

Inda bayan karewar wa’adin a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba 2023, kungiyar ta kara wa’adin mako guda domin bai’wa gwamnonin Jihohin Karin damar cika wannan buƙata, inda kuma wa’adin zai kare a gobe Laraba.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: