Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFFCC Abdulrashid Bawa ya shaki iskar ‘yanci daga hannun jami’an tsaron farin kaya na DSS, bayan shafe kwanaki sama da 100 a hannunsu.

 

Jaridar Punch ta tabbatar da sakin da DSS suka yi Bawa a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya a daren ranar Laraba.

 

An dakatar da Bawa ne domin a sami damar gudanar da cikakken bincike a kan zargin aikata almundahanar da ake yi masa.

 

DSS ta saki Abdulrashid Bawa ne bayan kammala bincike akan badakalar da ake yi masa.

 

Wani bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka saki Bawa yayin da aka gano shi tare da yan uwa da iyalansa.

 

DSS sun kama Bawa ne a ranar 14 ga watan Yuni shekarar da muke ciki, bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: