Rundunar ‘yan sandan birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da satar mazakuta.

 

Kwamishinan ‘yan sandan birnin Haruna Garba shine ya tabbatar da hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Laraba.

 

Kwamishinan ya ce wasu fusatattun matasa ne su ka hallaka mutumin mai suna Alhaji Tijjani Yakubu bayan dukan shi da suka yi, bisa zarginsa da suke da sacewa Emmanuel Danladi mazakuta a kauyen Kabusa da ke garin na Abuja.

 

Haruna ya kara da cewa bayan samun labaran faruwar lamarin, jami’ansu suka kama wanda ake zargi da hallaka mutumin kan zargin satar mazakuta.

 

Kazalika ya ce bayan daukar wanda ake zargin aka mikashi zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

 

Kwamishinan ya kara da cewa an mika Emmanuel Asibiti domin bincikar mazakutar ta shi, inda aka tabbatar da babu abin da ya same ta.

 

Sannan ya ce Emmanuel da wasu mutane biyu da ake zargi su na hannunsu kuma da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: