Jami’an rundunar sojin Najeriya sun hallaka ‘yan boko haram biyar tare da kama daya a daren ranar Laraba a garin Geidam da ke karamar hukumar Geidam ta Jihar Yobe.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’an sun kwato bindigogi kirar AK-47 da dama tare da babura.

 

Wani mazaunin yankin ya shaidawa Daily Trust cewa mazauna yankin sun cika da fari ciki bisa nasarar da jami’an suka samu, bayan da ayyukan mayakan na boko Haram a garin ke kara karuwa a baya bayannan.

 

Mazaunin yankin ya bayyana cewa hare-haren na ‘yan ta’addan ya sanya manoma da dama a Jihar kauracewa gonakinsu sakamakon yawaitar haren-haren ‘yan ta’addan.

 

Ya kara da cewa koda a ranar Asabar da ta gabata sai da ‘yan ta’addan suka hallaka wani mai suna Usman Gombe a garin na Geidam.

 

A yayin harin ‘yan ta’addan da dama ne suka tsere dauke da raunuka.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: