Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane bisa zarginsu da hannu wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami a sassan jihar.

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce jami’an tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne a maɓoyar su da ke gonar Nuba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna da alhakin yin garkuwa da sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC a Kaduna, Kawu Yakassai a ƙaramar hukumar Soba a ranar 25 ga watan Agusta da kuma wani da aka kashe, Adamu Muazu kwanan nan.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin a matsayin Bello Suleiman, Ismail Abubakar, Usman Suleiman, Umar Suleiman, da Isah Lawal, dukkansu daga ƙauyen Farin Kasa da ke ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna.

Sauran sun haɗa da Abubakar Bello, Ibrahim Mu’azu da Umar Suleiman.
Hassan ya kuma bayyana cewa, shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutanen, mai suna Hanazuwa, ya tsere amma jami’an tsaro na cigaba da bin sawunsa, yayin da waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Haka zalika, kwamishinan ƴan sandan jihar, Musa Garba, ya yabawa jami’an da suka kama waɗanda ake zargin da yin garkuwa da mutanen, inda ya ɗora musu alhakin cigaba da sanya ido sosai a lokutan bukukuwan da ke tafe.