Gwamnatin jihar Gombe ta ƙudiri aniyar farfaɗo da wasan langa da kokawar gargajiya a tsakanin matasa domin dauke hankalinsu daga shaye-shaye.

 

Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Adamu Inuwa Ibrahim, ne ya shaida wa manema labarai hakan kan irin shirye-shiryen da suke da shi ga matasa a 2024.

 

Kwamishinan ya ce za su zakulo matasan da suke da baiwar iya wasanni musamman langa da kokawa da tsere da sauransu don ganin sun zamo masu amfani a tsakanin al’umma maimakon barinsu suna shaye-shaye a kan titi.

 

Ya ce gwamna ya ba su damar haɗa kai da ma’aikatar ilimi wajen dawo da martabar wasanni a makarantun sakandare da ke fadin jihar.

 

A cewarsa gwamnati ta kuduri aniyar yin hakan ne ta hanyar ware wasu kudade a kasafin kudin 2024 domin ganin an bunƙasa harkokin matasa wajen samar musu da sana’oi da kuma aikin yi baya ga wasanni.

 

Ya kuma ce gamsuwa da za a yi hakan ne ya sa wasu matasa sama da 50 suka gabatar da kansu a ofishin Kwamishinan ‘yan sanda suka kuma yi alkawarin taimakawa wajen hana barna a Gombe.

 

Sannan ya ce waɗanda ba sa zuwa makaranta za a samar da kwamiti da zai hada kai da hukumar wasanni wajen bi unguwa–unguwa ana zakulo su ana saka su cikin harkar wasanni sannan kuma a ga yadda za a yi su koma makaranta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: