Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya bayyana cewa bai haramtawa ma’aikatan Jihar sanya kayan gargajiya ba, da babban Riga a lokacin da za su tafi aiki.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Jihar, Ibrahim Bologi ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa,an yiwa kalaman da gwamnan yayi mummunar fahimta, akan sanya kayan, yayi tafiyar ma’aikatan zuwa guraren ayyukansu.

Sanarwar ta Kara da cewa gwamnan ya bai’wa ma’aikatan gwamnatin shawara ne akan zamo wa manoma, tare da cewa manyan manoma suma na yin shiga ta alfarma yayi tafiya gurin ayyukansu.

Kakakin ya ce mutane na sukar kalaman na Bago ne domin bata masa suna.
Ibrahim ya bayyana cewa a jiya Litinin ne dai mutane,su dauke bidiyon da Bago yayi tare da datsar wani guri daga ciki, inda gwamnan yake cewa, ya zama wajibi a daina sanya gargajiya zuwa office,daga farko sati zuwa karshen sati.
Inda Kakakin ya ce ba haka gwamnan yake nufi ba,kawai mutane sun dauki gurin ne su na yadawa domin batawa gwamnan su na.