Babban hafsan tsaron kasa Janar Christopher Musa ya bayyana cewa za a fitar da rahoton binciken da aka yi kan harin bom da aka kai’wa masu taron mauludi a Kaduna zai fito nan ba da dadewa ba.

Babban hafsan tsaron ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da gidan talabijin na Channels a ranar yau Talata.

Musa ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa da zarar rahoton binciken ya kammalu, za a bayyana shi kowa yasan musabbabin faruwar lamarin a kauyen Tudun Biri da ke Jihar ta Kaduna.

Christophe Musa ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin rundunar soji ta tsaya tsayin daka wajen ganin an gano abin ya hadda hakan akan masu taron mauludin.

Sannan ya kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike akan lamarin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: