Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da wasu masu gadin Asibitin Imam Wali bangaren mata da ke Jihar daga bakin aiki bisa samunsu da sakaci.

Gwamnatin ta dauki matakin dakatar da masu gadin ne ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin.
Dakatar da ma’aikatan na zuwa ne a lokacin da suka yi sanadiyar haihuwar wata mai juna biyu a cikin mota a gaban asibitin.

Babban sakataren hukumar kula da asibitoci na Jihar Kano Dr Mansur Nagoda ne ya tabbatar da sallamar mutanen ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Samira Sulaiman ta fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da masu gadin ne, a yayin da aka kawo matar Asibitin, yayin da mijin matar yake ta kwankwasa kofar asibitin, babu masu gadi a gurin wanda hakan yasa mijin daukar bidiyon faruwar lamarin sannan ya yada shi.
Hakan ne ya sanya Dr Nagoda ya amince da dakatar da masu gadin asibitin, tare da umartar samar da sabbin masu gadi tare da tura su gurin nan take.