Babban bankin Kasa na CBN ya ja kunnen masu sana’ar POS akan yadda ake kara samun karancin kudi a Kasar.

Daraktan yada Labaran bankin Sidi Ali ne ya yi gargadin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
CBN ya bayyana cewa akwai hadin baki tsakanin wasu bankunan ajiyar kudi da masu sana’ar ta POS, domin kawo cikas wajen yawaitar takardun kudi a Kasar.

Sanarwar ta kara da cewa matukar bankunan da masu POS din ba su daina boye kudaden ba za su fuskanci fushin hukuma.

Bankin na CBN ya bayyana hakan ne a lokacin da al’umma ke korafin Kara samun karancin takardun kudi a Kasar.
CBN ya kuma bukaci mutane da su ringa shigar da korafe-korafen ta kafar Internet,domin kawo karshen bangarorin biyu masu wannan dabi’a.