Yar gidan sheikh Ibrahim Zakzaky Suhaila wacce a halin yanzu take kasar waje, ta ce a cigaba da zanga-zanga har sai gwamnati ta sako mahaifinta.
A cewar Suhaila sanarwar da wani mai suna Ibrahim Musa ya fitar ta cewar wai Almajiran Mahaifin ta su dakatar da Zanga-zangar da suke yi, ba da yawun Ƙungiyar IMN yayi ba yayi ne kawai domin wata manufa ta kashin kansa ba wai da yawun Almajiran Malam ba.
Suhaila Zakzaky ta ce babu adalci ko kadan na tsare Mahaifin ta da gwamnatin Buhari ta yi, kuma mafita daya ce ita ce yin wannan Zanga-zangar domin tursasawa gwamnati sakin mahaifin na ta, saboda haka a daidai wannan gaba wani ya fito yace wai za’a dakata da yin Zanga-zangar da akwai lauje cikin nadi a lamarin.
Suhaila ta Tabbatar da cewa sakin iyayenta biyu Zakzaky da Zeenatu shine kawai zai dakatar da wanna zanga-zanga
#punch

Leave a Reply

%d bloggers like this: