Wasu mutane uku sun rasa rayukansu daya ya kubuta bayan kasa ta zaftare da su A Jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a Unguwar Ayaba da ke karamar hukumar Keffi ta Jihar.


Wadanda suka rasa rayukan sun kasance Leburori, inda suke hako kasa su na zubawa a cikin mota wanda hakan ya sanya kasar ta zaftare tare da rufta musu.
Bayan faruwar lamarin masu aikin ceto da mutanen kauyen sun isa gurin domin dakko wadanda abin ya faru akansu wanda hakan ya gagara.
Mutanen garin sun bayyana cewa ba za su bar gurin ba har sai an dakko gawar mutanen.
Sannan sun ce an aike da wanda ya kubuta zuwa asibiti domin bashi kulawar gaggawa a kan raunukan da ya samu.