Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta kama wani bakanike bisa zargin satar wata mota

Kakakin rundunar ‘yan sanda Jihar Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.


Kakakin ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan mai motar ya shigar da kara a ofishin ‘yan sandan kancewa an sace masa mota.
Ya kara cewa wanda ake zargin ya je gidan wanda ya dauke masa motar, inda ya karbi mukullin motar a gurin ‘yarsa bayan ya tafi coci a ranar Lahadi sannan ya tsere da ita.
Kakakin ya ce bayan shigar da korafin a yau Litinin baturen ‘yan sandan yankin da lamarin ya faru ya tura jami’ansa, har ta kai ga sun samu nasarar kama wanda ake zargin bayan sayar da ita ga wani mutum.
A cewar kakakin an kuma kama wanda ya sayi motar, tare da ci gaba da gudanar da bincike akansu.