Rahotanni daga Jihar Filato na nuni da cewa bayan sanya dokar hana fita da gwamnatin Jihar ta yi na sa’o’i 24 a jiya Talata, ‘yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare a karamar hukumar Mangu ta Jihar a safiyar yau Laraba.

Hare-haren na yau Laraba yayi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a kauyen Kwahaslek da ke cikin karamar hukumar ta Mungu.
Mazauna garin sun bayyana cewa zuwan ‘yan bindigar ke da wuya suka bude wuta akan mutanen kauyen.

Shi ma wani mazaunin kauyen mai suna Sulaiman Muhammad ya bayyana cewa ‘yan bidigar sun je ne da misalin karfe 9:30am na safiya inda suka budewa mutanen yankin wuta tare da kone gidaje da dama cikin harda wata makarantar islamiyya.

Sulaiman ya kara da cewa mafiya yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu mata ne da kananan yara.
Idan ba ku manta ba dai a jiya Talata mun baku labarin cewa gwamnatin Jihar ta Filato ta sanya dokar hana fita na tsawon 24 a kuyen na Mangu, da nufin dakile hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankuna na Jihar inda kuma kafin karewar wa’adin dokar ‘yan bindigar su kakai hari kauyen.