Majalisar dokokin jihar Ondo ta tantance tare da tabbatar da Olayide Adelami a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo.

Wannan na zuwa ne a yau Alhamis sa’o’i 24 bayan gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ya zaɓi Adelami a matsayin mataimakin gwamna, kuma ya aika sunansa ga majalisar domin tantancewa da amincewa da shi.
Majalisar ta tabbatar da wanda aka naɗa ne bayan nazarin rahoton kwamitin zaɓen majalisar wanda shugaban majalisar, Mista Olamide Oladiji ya jagoranta a yayin zaman majalisar.

Tun da farko majalisar ta gudanar da aikin tantance wanda aka naɗa a harabar majalisar kafin zamanta.

A yayin zaman majalisar, maga takardar majalisar Jaiyeola Benjamin ya karanta wasiƙar da gwamna Aiyedatiwa ya aike wa majalisar domin tantance wanda aka naɗa.
Shugaban majalisar, Oladiji wanda ya yanke hukuncin tabbatar da wanda aka naɗa, ya taya mataimakin gwamnan murna, inda ya buƙace shi da ya yi iya bakin ƙoƙarinsa.
Ya kuma yi alƙawarin goyon bayan majalisar ga ɓangaren zartarwa domin jama’ar jihar su ci moriyar dimokuraɗiyya.
A nasa ɓangaren, Adelami ya yabawa Gwamna Aiyedatiwa kan naɗin da ya yi masa, inda ya yi alƙawarin ba zai ci amanar amincewar da aka yi masa ba.