Kotun Ƙoli da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun dukaka ƙara da ta yankewa tsohon dan Majalisar Wakilai Faruk Lawan hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru Biyar sakamakon kamashi da karbar cin hanci dala 500,00 daga hannun wani dan kasuwa kuma shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited Femi Otedola.

Alkalin kotun mai shari’a John Okoro, ya yanke hukuncin ne a yau Juma’a kamar yadda mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanto inda kotun ya tabbatar da hukuncin kotun baya.


A yayin yanke hukuncin Kotun mai alkalai biyar karkashin Okoro, ta ce dan majalisar ba shi da wasu ingantattun hujjojin da ya gabatarwa da kotun.
Daukaka karar da dan majalisar ya yi, ya nemi da kotun ta kolin ta soke hukuncin kotun daukaka karar, wanda ta yanke masa tun a ranar 24 ga watan Fabrairu 2022.
Tun a shekar 2021 ktun ta bayar da umarnin tsare tsohon dan majalisar, inda kuma a shekarar ta 2022, kotun daukaka kara ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar, a kan zarge-zarge Biyu daga cikin ukun da ake yi masa.
Daga cikin zaege-zaegen sun hada da cin hanci da Rashawa da gwamnatin tarayya ke yi masa.