Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta ci gaba da biyan naira 35,000 matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

Hakan na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago NLC ke shirin tafiya yajin aiki tare da buƙatar a mayar da mafi ƙarancin albashi naira miliyan guda.


Ƙaramar ministar ƙwadago Nkeiruka Onyejeocha ce ta tabbatar da haka a wani zama da su ka yi da shuwagabannin ƙungiyar yau a Abuja.
Ƙungiyar ta shirya tafiya yajin aikin makonni biyu ganin yadda gwamnatin ƙasar ta gaza cika alkawuran da ta ɗauka musu a shekarar da ta gabata.
Ƙaramar ministar ta tabbatarwa daa ƙungiyar cewar gwamnatin na iya kokarinta wajen ganin ta cika alkawuran da ta ɗauka.
Idan ba a manta ba a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne gwamnatin da ƙungiyar su ka cimma matsaya a kna abubuwa 16 ciki har da mafi ƙarancin albashi naira 35,000.