Hukumar jin daɗin alhazai a jihar Jigawa ta ce mutane 1,200 ne su ka biya kuɗin aikin hakkin bana daga cikin gurbin mutane 1,518 da hukumar aikin hajji ƙasa ta basu.

 

Mai magana da yawun hukumar Alhaji Murtala Usman shi ya bayyana hak ayayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Dutse babban birnin jihar

 

Ya ce mutane 1,200 kaf cikinsu sun kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana.

 

Ya ce zuwa yanzu sun mayar da hankali wajen yadda za aa fara shirya bita da wayar da kan maniyyatan don gudanar da ibada karbabbiya.

 

Hukumar ta shawarci maniyyatan da su halarci dukkan bitar da aka shirya ganin yadda ta ke da muhimmnaci.

 

A iya cewa fiye da kashi 70 na gurbin mutanen da hukumar aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta baiwaa jihar Jigawa sun kammala biyan kuɗin kujerarsu zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: