Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun bayyana cewar akwai wasu mutane da su ke ɗaukar nauyinsu.

 

Mutanen sun bayyana haka ne bayan da hukumar kare fararen hula ta samu nasarar kamasu a ranar Litinin.

 

Yayin da yake holen mutane da dama da aka kama masu laifi daban daban, kwamandan hukumar Olusola Odumosu ya ce sun samu nasarar ne haɗin gwiwa daa jami’an soji da jami’an tsaron DSS.

 

Sannan sun kama mutane 42 daga ciki akwai masu fakewa da harkar ma’adanai.

 

Ƴan bindigan na cikin daajin Tsauni iyaka da Lambata da ke ƙaramar hukumar Gurara ta jihar Neja.

 

Matasan sun shaida musu cewar su na aikata ta’addancin ne a jihohin Zamfara, Kogi da jihar Neja.

 

Sannan akwai wasu da su ke ɗaukar nauyinsu kamar yadda su ka shaida.

 

Kwamandan ya ce tuni bincike ya yi nisa kuma da zarar sun kammala za su bayyana halin da kae ciki a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: