Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun hallaka mutane biyu da jami’an yan sanda biyu sannan su ka yi garkuwa da wasu mutane 40.

 

Lamarin ya faru a Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

 

Al’amarin ya faru a jiya Talata kamar yadda wani Abubakar Kaura ya shaida.

 

Ya ce ƴan bindigan sun shida dauka da muggan makamai yayin da su ka yi wa garin tsinke.

 

Sannan sun yi garkuwa da mata da jikokin shugaban ƙungiyar direbobi ta jihar Hamisu Kasuwar Daji.

 

Haka kuma an hallaka jami’an yan sanda biyu yayin da su ka kai hari ofishinsu da ke kusa da garin.

 

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Sai dai ya ce har yanzu ba su iya tantance adadin mutanen daa aka yi garkuwa da su ba.

 

Kuma tuni aka aike daa jami’an yan sanda da soji gari domin cigaba da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: