Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar lll ya nuna tsoro dangane da halin da ake ciki na yunwa a ƙasar wadda ke ɗauke da miliyoyin matasa marasa aikin yi.

Sarkin ya yi jawabin ne a taron kwamitin zaartarwa na shugabannin gargajiya na arewa wanda ya gudana a Kaduna ranar Laraba.


Ya ce matsin tattalin arziki da wahala da ƴan ƙasar ke ciki babbar barazanace kuma hakan ya sanya mutanen a cikin fushi.
Haka kuma ya magantu dangane da batun tsaro wanda ya ce a wannan lokaci wasu gwamnonin sun koma kan kujerarsu yayin da wasu su ka samu dama a karon farko.
Sarkin ya ce mafi yawan mutane a yanzu ba sa iya ciyar da kansu saboda wahala daa tsadar rayuwa.
Batun rashin tsaro da ƙaruwar talauci abubuwa ne masu girman gaske da ya kamata shuwagabanni su yi duba a kansa.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga gwamnoni da su haɗa kai da shuwagabannin gargajiya domin magance matsalar tsaro a jihohinsu.
Sannan ya yi gargadi don ganin an samarwa matasa aikin yi, domin a cewarsa matuƙar aka bar matasa babu aikin yi kuma babu abinci ga talauci, to kuwa lallai akwai gagarumar matsala a nan gaba.