Hukumar kula da man fetur ta kasa a Najeriya NUPRC na duba yuwuwar mayar da wani ɓangare nata zuwa jihar Legas.

 

A wata takarda mai dauke da sa hannun Dakta Kelechi Onyekachi Ofoegbu a madadin shugaban.

 

Hukumar ta ce za ta yi hakan ne bisa yadda ake kashe kuɗaɗe masu yawa wajen zirga-zirga daga Legas zuwa Abuja.

 

Takardar mai ɗauke da kwanan watan 14/2/2024, hukumar ta ce hakan zai taimaka mata wajen samun nasarar gudanar da ayyukanta.

 

Sannan sun buƙaci kowanne bangare na hukumar ya bayar da adadin mutanen da ke wajen domin duba mutanen da za a sauya musu wajen aiki zuwa Legas.

 

Hukumar ta sanya ranar Juma’a 23 ga watan Fabrairu domin kammala aikin tantancewa da karɓar ɓangarorin don cigaba da ayyukansu.

 

Idan ba a manta ba a baya, hukumar kula da jiragen sama ta FAAN da babban bankin Najeriya CBN sun ayyana sauya wasu ɓangarori daga cikinsu daga Abuja zuwa Legas, wanda hakan ya jawo cece ku ce a tsakanin yan ƙasar musamman arewaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: