Mutane shida aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka jikkata goma a sabon harin da ƴan bindiga su ka kai jihar Katsina.

Ƴan bindigan haye kan babura sun shiga ƙauyen Yar Nassarawa da ke ƙaramar hukumar Faskari a Katsina.


Bayan kisan mutanen sun yi garkuwa da wasu da ba a kai ga gano adadinsu ba.
Ƴan bindigan sun shiga tsakar daren jiya Litinin wayewar yau Talata sannan su ka yi wa ƙauyen kawanya.
Baya ga haka sun sake kai hari ƙauyen Ruwan Godiya da ke ƙaramar hukumar Faskari tare da awon gaba da dabbobi masu yawa.
Mai magan da yawun ƴan sanda a jihar Saddiƙ Abubakar ya tabbatar da faruwar haka a wata sanarwa da ya fitar yau Talata.
Ya ce an kashe mutane shida kuma an jikkata goma sanna an ƙone gidaje uku da babura goma.
Tuni kwamishinan ƴan sanda a jihar ya bayar da umarni ga kwararrun jami’ai don ganin an kama waɗanda su ka kai harin.