A yammacin jiya Talata wasu ƴan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto tare da yin garkuwa da mutane 26.

An yi garkuwa da matafiyan bayan tare babbar hanyar a ƙauyen Kwaren Kirya da ke karamar hukumar Maru ta jihar.


Mutane a yankin sun tabbatar da cewar lamarin ya kazanta domin ƴan bindigan na tare hanyar tare da yin garkuwa da mutane a kowacce rana.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa talabijin channels cewa a yammacin yau sun tare mota mai daukar mutane 18 da kuma wata kirar Golf.
Kuma ya zargi mutanen wani ƙauye mai suna Balge da cewar akwai masu garkuwa a ciki.
Ya ce fiye da kashi 80 na mutanen ƙauyen masu garkuwa da mutane ne.
Sannan ya yi kira ga gwamnati don ganin ta zuba jami’an tsaro a yankin tare da kafa shingen bincike don sa ido a kan gudanarwar lamura.