Ƙungiyar masu motocin dakon man fetur ta Najeriya sun ce buƙatar da su ka nema daga gwamnatin tarayya ba zai shafi ƙari ko ragin man fetur ba.

Ƙungiyar ta dakatar da ayyukanta a ranar Litinin bisa asara da shugaban ta ce su na yi.
Sai dai sun dawo bakin aiki jiya Talata bayan da aka amince da kara musu kuɗin dakon mai da aka ki yi tun tuni.

Shugaban kungiyar na kasa ya bayyana yau a gidan talabiji na channel cewa, bukatun da su ka nema ba zai shafi farashin man fetur ba, domin daga abinda su ka nema kyautatawa ne da sadaukarwa daga dillalan man fetur.

Ya ce idan aka yi duba motocin da su ke dakon mai da su gas su ke zuba musu, kuma ga farashin da gas yake a yau.
A baya ya ce a kowacce mota idan su ka yi dako su na asarar sama da naira dubu ɗari wanda hakan ya tilasta su ka jingine ne motocinsu.
Sai dai a yanzu sun koma bakin aiki bayan da aka amince da ƙara musu farashin dakon man.