Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta roƙi ƙungiyar kwadago da ta janye shirin zanga-zanga da ta shirya yi a ranakun 27 da 28 na watan da mu ke ciki.

Mai magan da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya bayyana yau a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Hukumar ta roƙi ƙungiyar don ta janye zanga-zangar ne saboda yanayin tsaro da kuma tattalin arziƙi.

Ƙungiyar ta bai wa gwamnatin kwanaki 14 don cika alƙawuran da ta ɗauka amma ta gaza.

Hukumar ta buƙaci ƙungiyar su tattauna da gwamnati don samar da masalaha maimakon zanga-zanga da su ka shirya yi.
Ƙungiyar ta zargi gwamnatin da gaza cika alkawuran da ta ɗauka tun a shekarar da ta gabata kan ƙarancin albashi da wasu buƙatunsu.
A baya, gwamnatin ta gana da ƙungiyar har ma ta bayyana aniyar cigaba da biyan naira 35,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
A sakamakon matakin da ƙungiyar ta ɗauka ne hukumar tsaro ta DSS ke rokon su janye daga aniyar yin zanga-zangar duba ga halin da ƙasar ke ciki.