Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta musanta labarin yin garkuwa da wasu ƴan bindiga su ka yi a hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Sai dai yan sandan sun tabbatar da cewar yan bindigan sun tare babbar hanyar a jiya Talata.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Yazid Abubakar ya tabbatar da cewar yan bindigan sun tare babbar hanyar sai dai ba su ɗauki kowa ba.

A jiya mun kawo muku labarin cewar yan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto tare da sace mutane 26 waɗanda matafiya ne.

A cewarsa, sun samu labarin ne da misalin ƙarfe tara na dare kuma sun yi ƙoƙarin daƙile harin yayin da jami’an yan sanda su ka yi musayar wuta da ƴan bindigan.
Sai dai wani da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce ce yan bindigan na tare mutane a babbar hanyar a kowacce rana, har ma ya zargi mutanen wani ƙauye Balge da cewar fite da kashi 80 ƴan bindiga ne.
Ya ce ko a yammacin jiya sai da ƴan bindigan su ka tare mota mai ɗaukar mutane 18 da wata mota kirar Golf tare da sace mutanen ciki.
A cewar yan sanda sun kori ƴan bindigan da misalin ƙarfe tara na dare yayin da su ka gudu ɗauke da raunin harbi a jikinsu.