Wasu da ba a san ko su waye ba sun kwashe kayan abinci da aka dakko a wata babbar mota a jihar Neja.

Al’amarin ya faru yau a yankin Suleja na jihar Neja.


Wani shaida da lamarin ya faru a gabansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar, mutanen sun tare babbar hanyar ne bayan da manyan motocin su ka dakko kayan abinci da nufin zuwa Kaduna.
An kona tayoyi a hanyar dalilin da ya baiwa mutanen damar kwasar kayan abincin.
Ya ce an kwace buhun shinkafa da dama.
A wani bincike ya nuna cewar matuƙa babur mai ƙafa biyu da aka fi sani da achaba na shirin yin zanga-zanga a jiya, sai dai ba a kai ga gano dalilin da ya sa hakan ba ta faru ba.
Jami’an soji sun yi harbe-harbe bayan da su ka isa wajen domin tarwatsa masu ɗaukar kayan abincin.
Idan za a iya tunawa, matasa a jihar Oyo sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa, hauhawar kayan abinci wanda ya zama gama-gari a Najeriya.