Jami’an tsaron ƴan sanda da hukumar tsaron fararen hula a Filato sun kai ɗauki bayan da wasu bata gari su ka yi yunkurin balle kasuwar kayan abinci.

Matasan da ba a san ko su waye ba sun yi yunkurin fasa katafariyar kasuwar kayan abinci ta Yankalli tare da sace kayan abinci.


Maza sa mata sun farwa kasuwar ne da misalin ƙarfe 08:00pm na daren jiya Juma’a.
Wani shugaban yan kasuwa a jihar mai suna Alhaji Jamilu Kabiru ya tabbatar da faruwar haka wanda ya ce sun yi gaggawar samarwa da jami’an tsaro.
Yaa ce tun daa farko sun samu labari cewar wasu bata gari za su farwa kasuwar tare da sace kayan abinci.
Sai dai ya yi mamaki ganin yadda kasuwar ke daidaita farashi wanda hakan ya sa mutane ke shige da fice don yin siyayya a ciki.
Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar haka, wanda ya ce tuni jami’an tsaro su ka kai ɗauki tare da daƙile yunkurin.