Bayan biyan naira miliyan 20 ƴan bindiga sun kashe guda cikin wanda aka biya kuɗin fansarsu a Abuja.

 

An yi garkuwa da mutane Bakwai a yankin Kaduru da ke Abuja a ranar 28 ga watan Disamban shekarar da ta gabata.

 

Bayan yin garkuwa da mutanen, yan bindigan sun buƙaci a basu kuɗin fansa naira miliyan 290.

 

Wani mazaunin garin ya shaida cewar yan bindigan sun kirasu jiya Juma’a tare da shaida musu cewar sun kashe guda cikin waɗanda su ka kama.

 

Sannan su ka yi barazanar hallaka sauran mutanen muddin ba su cika musu kudin da ya kai naira miliyan 230 ba.

 

Daga cikin mutanen da ke tsare hannun ƴan bindigan akwai mace mai juna biyu da maza biyu sai ƙananan yara guda biyu da jaririn watanni.

 

Bayan tuntubar jami’an yan sanda a Abuja sun ce ba su da masaniya dangane daa haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: