Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buɗe iyakokin ƙasar na ƙasa.

Gwamna Abba ya miƙa buƙatar ne yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban hukumar hana fasa ƙauri ta ƙasa kwastam yau Litinin a ofishinsa.
Gwamna ya ce hahawar kayan masarufi da stadar kayayyaki ta haifar da yunwa a Najeriya.

Haka kuma gwamnan ya buƙaci shuagan Najeriya ya samar da wata hanya da za a taimakawa ƴan Najeriya don rage raɗaɗin yunwa da ae fama da ita.

Ya ce baya ga tallafi na musamman tare da hanyoyin da gwammatin tag a dacewar bi don sauƙaƙa yunwa, akwai buƙatar buɗe iyakokin ƙasar don wadata ƙsar da abinci.
Dangane da watan Azumin Ramadan, gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duba a kai tare da samar da wata hanya don tallafawa jama’a.
Daga ƙarshe gwamnan ya jadda cewar a shirye yake don bayar da dukkanin goyon bayan da ake buƙata daga gareshi don samun nasarar hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya.
