Majalisar dokokin jihar Katsina ta lashi takobin kakkabe dukkanin ƴan bindigan da ke jihar.

Shugaban majalisar Shamsudden Abubakar Dabai ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da gidan talabiji na Channels.
Ya ce majalisar za ta yi duk mai yuwuwa don ganin ta kakkaɓe ƴan bindiga a Katsina da masu ɗaukar nauyinsu.

Ya ce a shirye majalisar ta ke don yin aiki hannu da hannu da gwamnan jihar don ganin an kawar da su daga jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Shamsudden Dabai ya ce su na buƙatar kowa ya bayar da gudunmawarsa don haɗa hannu ta yadda za a samu nasara a kai.
Jihar Katsina, wadda ke fama da hare-haren ƴan bindiga, sai dai gwamnan jihar ya ce a shirye yake don ganin an kawo ƙarshensu.
An samu hare-haren da su ka yi silar rasa rayuwa da dukiyoyin mutane da dama a jihar sakamakon ayyukan masu garkuwa da sauran masu aikata laifuka.
