Aƙalla mutane Bakwai ne su ka rasa rayuwarsu a wani hari da ka kai wata kasuwa a Filato.

An kashe mutanen a wata kasuwa da ke ƙaramar hukumar Wase ta jihar yau Litinin.

Wani shugaban matasa a yankin Abdullahi Hussaini ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai, wanda ya ce ƴan bindigan sun shiga kasuwar da misalin ƙarfe 2pm na rana sannan su ka buɗewa mutane wuta.

Yaa ce ƴan binddogan haye kan babura, sun jikkata wasu da raunin harbi.

Daga bisani ƴan bindigan sun tsere zuwa cikin daji.

A cewarsa, an aike da jami’an ƴan sanda a yankin domin tabbatar da doka da oda da kuma zaman lafiya.

Daga ɓangaren ƴan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin a Zuraj Compani, wanda mai magana da yawunsu ya ce mutane huɗu ne su ka mutu yayin da shida su ka jikkata.

Sai dai mutane a yankin sun buƙaci a ƙara yawan jami’an tsaro saboda fargabar abinda ka iya zuwa ya komo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: