Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da bude iyakokin kasar wadda ta hada Najeriya da Nijar.

 

Mai magana da yawun shugaban kan yada Labarai Ajure Ngelale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

 

Ngelale ya ce daukar matakin bude iyakokin na zuwa ne bisa shawarwarin da shugabanni kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta ECOWAS suka bayar a gurin taron da suka gudanar tun a ranar 24 ga watan Fabrairu.

 

Ajuri ya ce umarnin na shugaba Tinubu zai shafi dukkan iyakokin da ke Sama da Kasa, tare da cire dukkan wani takunkumi da aka sanyawa Nijar.

 

Bude iyakokin Kasar na zuwa ne a lokacin da ‘yan kasar ke ta kiraye-kirayen bude bodojin Kasar baki daya, domin samun saukin shigowa da kayayyaki daga waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: