Gwamnatin Jihar Osun ta gano shirin ‘yan ta’adda na kai hare-hare wasu yankuna a Jihar.

 

Gwamnan Jihar Ademola Adeleke ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawusa Olawale Rasheed ya fitar a ranar Talata.

 

Gwamnan ya bayyana cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-haren ne a Makarantu da gonakin manoma a kauyukan Jihar.

 

Adeleke ya kara da cewa sun gano shirin na batagarin ne ta cikin wani bayannan sirri da aka tattara akai.

 

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na shiga damuwa bisa samun wadannan bayanan akan maharan da suke kokarin yin garkuwa da mutane da kuma tarwatsa amfanin gona.

 

Kazalika gwamnan ya ce maharan na kuma yunkurin sace dalibai a makaratu ne domin kawo nakasu a makarantun Jihar.

 

Gwamnan ya kara da cewa bayan samun bayanan ya kira taron majalisar tsaro domin tattaunawa akan lamarin.

 

Gwamnan ya kuma yi kira ga makarantu da su dauki matakan kariya domin gujewa sace daliban makarantun.

 

Daga karshe gwamnan ya umarci Kwamitin samar da abinci da ya gabatar da bayanin wucin gadi, domin bayar da kariya ga gonaki da kuma manoma baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: