Majalisar wakilai a Najeriya ta kafa kwamitin da zai gayyaci shugabannnin kamfanonin sarrafa siminti ciki har da Dangote da BUA.

Hakan ya biyo bayan ƙudirin Jonathan Gaza, guda cikin mambobin majalisar.
Matakin na zuwa ne bayan da aka samu ƙarin farashin da kaso %100 cikin watanni uju.

Majalisar ta gano cewar a wata uku baya, ana siyar da buhun siminti naira 5,000, yayin da a yanzu yake naira dubu goma 10,000.

A watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta gana da shuwagabannin masu kamfajin siminti na ƙasarwanda su ka yi alƙawarin sakko da farashinsa zuwa naira 7,000 ko 8,000 amma har yanzu ake siyarwa naira 10,000.
Majalisar ta kafa kwamitin da zai gayyaci manyan shugabannin masu kamfanin sarrafa siminti a Najeriya, domin yin bayani kan abinda ke faruwa ba a samu ragin farashin ba.
